Sojojin Habasha sun kashe mayakan sa kai 150 a Amhara

Sojojin Amhara, Habasha, kashe, mayakan, sa kai
Rundunar sojin Habasha ta bayar da rahoton cewa, sojojin ƙasar sun samu nasarar dakile wani hari da mayakan Fano suka kai a Tis Abay, kusa da babban birnin...

Rundunar sojin Habasha ta bayar da rahoton cewa, sojojin ƙasar sun samu nasarar dakile wani hari da mayakan Fano suka kai a Tis Abay, kusa da babban birnin yankin Amhara, Bahir Dar, wanda ya yi sanadin mutuwar mayakan sa kai sama da 150.

A sakon da rundunar ta wallafa a shafin Facebook ta bayyana harin a matsayin takamaimai, wanda ya tilastawa mayakan ja da baya tare da yin watsi da gawawwakinsu da makamai.

Karin labari: Shaguna 180 sun ƙone a gobarar babbar kasuwar Sokoto

Kafin wannan matakin na rundunar, Fano ya tabbatar da iko da Tis Abay a ranar 16 ga watan Maris.

Sai dai fadan da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojoji da mayaƙan Fano a yankin Amhara ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula, kamar yadda kafafen yada labarai na ƙasar suka rawaito, lamarin da ke nuni da rikicin da aka dade an fama da shi a yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here