Allah ya yi wa Omar Farouk, dan Hakimin Dambatta kuma Sarki Bai na Kano, Dakta Mansur Mukhtar rasuwa.
Mukhtar, mahaifin marigayin, tsohon ministan kudi ne.
Iyalan marigayin ne suka bayyana hakan a wata sanarwa da suka fitar ranar Lahadi a Abuja.
Farouk ya rasu ne a ranar Asabar a Abuja, kuma an yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan an yi masa addu’a a masallacin kasa. (NAN)













































