Osinbajo ya bar Abuja zuwa birnin Landan domin halartar Jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu

Osinbajo Depart
Osinbajo Depart

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bar Abuja ranar Asabar zuwa birnin Landan.

Ana sa ran Osinbajo, zai wakilci Najeriya a wajen jana’izar marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ne ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitterranar Asabar.

Sakon yace Osinbajo, zai hadu da Sarki Charles, da dangin sarki da sauran shugabannin duniya a wasu tarurruka da liyafar da suka hada da taron kasashen biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here