NNPP ta sha alwashin dakile duk irin abin da faru a zabukan 2019

IMG 20221012 WA0247
IMG 20221012 WA0247

Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar NNPP Abba Kabiru Yusuf ya sha alwashin yin dakile duk wani kamar yadda yadda wakana a zaben shekarar 2019 da aka bayyana bai kammala ba..

Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya bayyana haka ne ta bakin kakakin sa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano, inda ya bayyana cewa, Abba Kabir-Yusuf, ya kammala shirye-shiryen bayyana tsare tsaren sa a hukumance ga jama’a da kuma kaddamar da kwamitocin yakin neman zaben sa a matakin jiha.

Ya ce jam’iyyar za ta yi dukkan mai yiwuwa ta hanyar doka, dan tabbatar da an dakile kura-kurai dasuka wakana a zaben 2019.

“A wannan karon, ba za mu laminci duk wani nau’i na tsoratarwa daga kowane bangare ba yayin da muke ta gwagwarmaya kan tsarin dimokuradiyya tare da gudanar da ayyukanmu cikin iyakokin da dokar zabe ta 2022 ta bamu dama” in ji shi.

Bature ya yi nuni da cewa, shugabannin jam’iyyar na jihar suna da cikakkiyar masaniya kan irin yadda ‘yan siyasa ke karbar katin zabe na dindindin daga masu son kada kuri’a a kokarinsu na hana su gudanar da ‘yancinsu na al’umma.

“Jam’iyyar mu tayi tanadin hanyoyi don bin diddigin rahoto da kuma bin diddigin shari’a kan duk wani mutum ko kungiyar da aka samu da aikata wannan danyen aikin da ya saba wa dokar kasa”.

“Yanzu haka dai a ranar 12 gawatan Oktoba ne, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta sanar da bude kamfen na dukkanin gwamnoni da na majalisun jihohi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here