NANS ta baiwa gwamnatin tarayya  wa’adin mako guda domin warware yajin aikin ASUU

NANS protest
NANS protest

Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta bayar da wa’adin mako guda ga gwamnatin tarayya da ta warware rashin jituwar da ke tsakaninta da kungiyar malaman jami’o’i ASUU ko kuma dalibai su tsunduma zanga-zanga a fadin kasar nan.

Shugaban kungiyar daliban, Sunday Adedayo, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, a Sokoto, jim kadan bayan sanya hannu kan kundin tsarin mulkin kungiyar da aka yi wa kwaskwarima a fadar gwamnatin jihar Sokoto.

Ya bayyana a matsayin abin takaicin yadda gwamnatocin kasar nan tun daga shekarar 1999 har zuwa yanzu suka kasa samun daidaito da ASUU.

Ya koka da yadda gwamnati ta yi watsi da harkar ilimi tun daga matakin Firamare da Sakandare kuma NANS ba za ta zuba ido tana kallon yadda gwamnati ke lalata ilimin manyan makarantu ba.

Kungiyar ta NANS ta je Sokoto ne domin taron duba tsarin mulki inda kungiyar ta duba kundin tsarin mulkin ta na tsawon shekaru arba’in a jami’ar jihar Sokoto.

Da yake jawabi tun da farko, Gwamna Tambuwal ya roki ASUU da su nemo hanyar warware sabanin da ke tsakaninsu ba tare da sun shiga yajin aikin ba.

Gwamna Tambuwal ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samo hanyar biyan bukatun ASUU duk da cewa kasar na fuskantar kalubalen tattalin arziki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here