Ma’aikatar Harkokin Mata ta Tarayya ta gudanar da taron farko na saka hannun jari tsakanin Najeriya da ƙasar China a birnin Beijing, a ranar Juma’a.
Wannan taron dai na da nufin jawo hankalin masu saka jari daga ƙasar China domin tallafa wa ayyukan da za su ƙarfafa mata a Najeriya.
Ministar Harkokin Mata da Jin Dadin Jama’a, Hajiya Imaan Suleiman Ibrahim, ta bayyana cewa taron ya yi daidai da manufofin shirin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda), inda ma’aikatarta ke da burin ƙarfafa mata miliyan goma domin taimaka wa ci gaban tattalin arziƙin ƙasar zuwa dalar Amurka tiriliyan ɗaya.
Taron mai taken “Mata a zuciyar gine-gine: Amfani da tsarin da ke da la’akari da mata don ci gaba mai ɗorewa da ƙarfafa zamantakewa” ya maida hankali kan tallafawa muhimman shirye-shiryen ma’aikatar, kamar Mata a Sashen Iskar Gas na Najeriya (WINGS) da kuma Faɗaɗa Aikin Mata a Noman Ƙasa (WAVE).
Shirin WINGS yana nufin bai wa mata damar shiga harkar makamashi tare da tallafa musu wajen canji zuwa amfani da makamashi mai tsabta, yayin da WAVE ke mai da hankali kan haɓaka rawar mata a harkar noma da kuma samun damar shiga kasuwanni da albarkatu.
Ministar ta bayyana cewa mata na da kaso kusan 70 cikin 100 na ma’aikata a fannin noma a Najeriya, amma har yanzu ana saka jari ƙalilan a cikinsu, abin da ke hana su samun ci gaba da dorewar kudin shiga.
Hajiya Imaan ta ce shirye-shiryen ma’aikatar na nufin buɗe sabon babi na ƙarfafa tattalin arziƙin mata ta hanyar samar musu da jari mai ma’ana, ƙara yawan halartarsu a harkokin tattalin arziƙi, da kuma gina sarkar samar da kayayyaki mai ɗorewa.
Taron ya samu halartar manyan jami’ai daga gwamnatocin Najeriya da ƙasar China, ciki har da shugabar kwamitin majalisar wakilai kan harkokin mata, Hajiya Kafilat Ogbara, inda suka tattauna kan hanyoyin haɗin gwiwa da damar saka jari don ƙarfafa ci gaban mata da ƙarfafa zamantakewa mai ɗorewa.













































