Mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon hatsaniya a Illorin

abdulrahman abdulrazaq
abdulrahman abdulrazaq

Ana fargabar mutane hudu sun rasa rayukansu ciki har da ’yan kungiyar asiri daban-daban, bayan da suka yi wata hatsaniya tsakanin su a Unguwar Olunlade, dake Ilorin, dai-dai lokacin da ake gudanar da bukukuwan bikin ranar 8 ga watan Agusta (8/8).

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ranar Talata a Ilorin.

Ya bayyana cewa alkaluman hukuma sun nuna mutuwar mutane biyu ne kawai a yayin bikin, amma mutanen yankin sun ce wasu kungiyoyin asiri sun kashe mutane hudu a wani harin ramuwar gayya.

Sai dai kakakin ya tabbatar da cewa an kashe mutane biyu a yayin da lamarin ya faru.

Okasanmi ya ce: “Mutane biyu ne kawai aka kashe a bikin na 8 ga watan 8 ba mutane hudu ba kamar yadda wasu mutane suka yi ta yayatawa.

Ya Kara da cewa mai yiwuwa abin da ya haifar da rikicin shi ne bikin ranar 8 ga watan Agusta kuma kungiyoyin asiri daban-daban na gudanar da bukukuwan ranar a wurare da dama a cikin garin.

Okasanmi ya tabbatar da cewa an shawo kan lamarin, inda ya kara da cewa an samu kwanciyar hankali a yankin.

Sai dai ya ce wani ma’aikaci a wata cibiyar gwamnati da ke yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce rikicin ya faro ne a daren ranar 8 ga watan Agusta, a wani gida da ke kusa da gidan mai na Bovas, Olunlade.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here