“Mun gano haramtattun matatun mai 84 cikin mako ɗaya” – NNPCL

NNPCL, haramtattun, matatun, mai
Kamfanin sarrafa albarkatun mai na Najeriya, NNPCL ya ce ya gano haramtattun matatun mai 84 da haramtattun bututan mai 66 cikin makon da ya gabata a yankin...

Kamfanin sarrafa albarkatun mai na Najeriya, NNPCL ya ce ya gano haramtattun matatun mai 84 da haramtattun bututan mai 66 cikin makon da ya gabata a yankin Neja Delta.

Cikin wani saƙo da NNPCL ya wallafa a shafin X, ya ce a makon da ya wuce, an gano haramtattun bututan mai 66 da haramtattun matatun mai 84 a yankin Neja Delta.

Satar ɗanyan mai babbar matsala ce a Najeriya, ɗaya cikin mambobin ƙungiyar ƙasashe masu arzikin mai kuma ɗaya daga cikin ƙasashen nahiyar Afirka mafi samar da arzikin mai.

Karin labari: “Babu wanda zai rasa aikinsa lokacin haɗe hukumomin gwamnati” – Mohammed Idris

Najeriya dai tana asarar kusan gangar mai dubu ɗari biyu a duk rana saboda masu haramtattun matatun mai da kuma masu satar man.

Galibin mutane a yankin Neja Delta na rayuwa cikin talauci duk da cewa ƙasar ce mafi samar da man fetur a Afirka inda ta ke samar da kusan ganga miliyan biyu duk rana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here