“Mun daina ɗaukar duk wani labarin da ya shafi gwamnatin Kano” – ‘Yan Jaridun Kano

'Yan jaridun, Kano, daina, daukar, labarin, gwamnatin
Ƙungiyar wakilan kafafen yada labarai (The Correspondent Chapel) ƙarƙashin Kungiyar ‘Yan jarida ta kasa NUJ a Kano ta ƙauracewa yaɗa duk wasu labarai da...
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Ƙungiyar wakilan kafafen yada labarai (The Correspondent Chapel) ƙarƙashin Kungiyar ‘Yan jarida ta kasa NUJ a Kano ta ƙauracewa yaɗa duk wasu labarai da suka shafi gwamnatin jihar Kano ba tare da ɓata lokaci ba.
Wannan mataki na zuwa bayan zargin cigaba da nuna halin ko’inkula ga mambobin kungiyar daga bangaren gwamnati da jami’an gwamnatin.

 

Karin labari: Hajjin Bana: “NAHCON za ta rage kwanakin da Alhazai ke yi a Saudiyya” – Jalal Arabi

Shugaban kungiyar Kwamared Aminu Ahmed Garko ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya aika wa manema labarai a kano, inda yace duk da ƙoƙari na ganin inganta dangantaka tsakanin ɓangarorin biyu abin ya ci tura, mambobin ƙungiyar na cigaba da fuskantar wulaƙanci da barazana a yayin da suke gudanar da ayyukansu.
A cewar Garko, “gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ba da fifiko ga ɓangaren waɗanda ba ƙwararru ba inda ake mayar da ƙwararun ‘yan jaridar da za su yi aiki saniyar ware.”

Karin labari: ‘Yan sanda sun farwa masu garkuwa da mutane tare da kama wasu a Abuja

Kungiyar ta umarci dukkanin mambobinta su mutunta wannan umarni wanda ya haɗar da rashin zuwa taruka na manema labarai da gwamnatin ke yi da tarukanta dama tattaunawa da jami’an gwamnatin ta Kano baki ɗaya.
A ƙarshe Ƙungiyar ta jaddada cewa gudanar da aikin jarida ba tare da katsalandan ba babban lamari ne a Dumokuraɗiyya da ake buƙatar ɗorewar sa, a don haka ba za ta zura idanu tana kallon mambobinta na fuskantar rashin mutuntawa ko fuskantar barazana ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here