Ɗan Majalisar Tarayya ya rabawa mutum 7 tallafin karatu Naira Dubu 250,000 ga duk mutum ɗaya

MB SHEHU
MB SHEHU

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Fagge Muhammad Bello Shehu ya rabawa ɗaliban da ke karatun ɓangaren Shari’a mutum 7 tallafin kuɗi Naira Dubu 250,000 ga duk mutum ɗaya.

Bikin wanda aka shirya a ƙaramar hukumar ta Fagge, yazo ne a daidai lokacin da ɗaliban ke neman ɗaukin tallafin karatun.

Karanta wannan: Cece-kuce: Kan kyautar motar Naira Miliyan 6 da Jaruma Fatima Hussaini ta samu

Manufar taron dai shi ne don tallafawa ɗaliban da suka kammala karatun shari’a daga Jami’o’i daban-daban ‘yan asalin ƙaramar hukumar da za su halarci makarantar koyon aikin lauya don cika sharuɗan zama barista wanda aka shirya a ƙaramar hukumar ta Fagge.

Wakilin mu ya rawaito mana cewa, waɗanda suka rabauta da tallafin dai sun haɗa da Salma Lawan Umar, da Mustapha Adam Abubakar, da Khalid Shitu Fagge, da Mubarak Sani Sa’eed, da kuma Ibrahim Sunusi Hassan, tare da Auwal Sani Muhammad.

Kazalika ɗaliban, sun bayyana farin ciki mara misaltuwa a gare su.

Barista Abba Hikima Fagge, lauya ne kuma masanin doka ɗan asalin ƙaramar hukumar, ya halarci bikin bayar da tallafin tare da nuna farin cikinsa.

“Gaskiya nayi matukar farin ciki da wannan biki da Muhammad Bello Shehu ya bawa ɗalibai mutum 7 tallafin karatu, haƙiƙa an ajiye ƙwarya a gurbinta tunda daman Shari’a ɓangarensa ne.

Karanta wannan: Gobara ta Lalata kasuwar Panteka dake Kaduna

Tabbas babu abinda za mu ce sai dai mu ƙara yiwa Allah godiya tare da yiwa wannan bawan Allah addu’ar ci gaba da ayyukan alheri a faɗin ƙaramar hukumar Fagge” A cewar Hikima.

Ya ƙara da cewa, ” Ni ƙofa a buɗe ta ke, ga duk wani ɗalibi mai son zama lauya, idan kuna son wata shawara ko wani abu da ya shige muku duhu, ku garzayo ofishina kai tsaye domin mu haƙa mu binne acikin gida ba tare da wani ma ya sani ba.” Inji Abba.

Shi ma a nasa jawabin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar ta Fagge Muhammad Bello Shehu, ya bayyana irin faɗi tashin da akayi har aka shirya wannan bikin bayar da tallafin.

Karanta wannan: Gwamnatin Kano za ta kashewa makarantun firamare 3 Naira Biliyan 8

“Alhamdulillah! wannan tallafi mun bawa ɗaliban ne don tallafa musu, haka kuma muna cigaba da zaƙulo zaƙaƙuran matasa masu son yin ƙaratu domin sa ke tallafa musu musamman ma waɗanda su ke koyon ilimin Shari’a” A cewar Shehu.

A ƙarshe dai al’ummar ƙaramar hukumar sun bayyana godiya da jindaɗin su tare da fatan alheri ga Ɗan majalisar ta Fagge.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here