Matuka baburin adaidaita Sahu sun Karrama Sanata Ibrahim Shekarau

IMG 20220806 WA0028 1068x801 1 750x430 1
IMG 20220806 WA0028 1068x801 1 750x430 1

A ranar Asabar ne kungiyar masu tuka baburin adaidaita sahu ta karrama Sanata Malam Ibrahim Shekarau, dake wakiltar Kano ta tsakiya a zauren majalisar Dattawan Kasar nan.

Tsohon Gwamnan Kano wanda ya yi wa’adi biyu a jere shi ne wanda ya bullo da baburin Adaidaita Sahu, a zamaninsa na farko.

Kungiyar masu sana’ar tuka baburin ta Kano ta tsakiya ne suka ba Shekarau lambar ta yabo a ranar Asabar.

Da yake jawabi a lokacin da yake ba da lambar yabo a madadin kungiyar, shugaban kungiyar, Nura Sabiu Umar, yace lambar yabon ta nuna godiya ga hangen nesa da ya yi na bullo da babur a lokacin yana Gwamnan jihar.

Ya ce bisa bullo da shirin, matukan sun samu damar biyan bukatun iyalansu na yau da kullum.

Da yake mayar da martani, yayin da yake karbar lambar yabo, Sanatan ya gode musu bisa karramawar da aka yi masa, ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, akwai sama da matuka baburin dubu 60 a fadin Kano, kamar yadda hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar, KAROTA ta bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here