Dakarun Operation Whirl Stroke da Safe Haven sun kama ‘yan ta’adda bakwai tare da kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su yayin wasu atisaye a jihohin Nasarawa da Filato da Kaduna.
Mai Magana da yawun rundunar Manjo Janar Bernard Onyeuko, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Juma’a.
Ta cikin sanarwar Onyeuko, ya ce sojojin sun ci gaba da mamayewa tare da hana masu aikata laifuka cin karensu babu babbaka a yankunan.
Onyeuko, ya kara da cewa tun a ranar 29 ga watan Yulin da ya gabata, sojoji sun gudanar da atisayen a kauyukan Akwana da Ayinbe da wasu kauyuka biyu dake karamar hukumar Logo a jihar Nasarawa.
Ya ce bayan musayen wuta, sojojin sun samu nasara akan Yan ta’addar inda suka gudu yayin da aka kama biyu daga cikinsu, Danladi Selfa mai shekaru 23 da Usman Ya’u mai shekaru 28.
Kazalika ya ce an kwace bindiga kirar AK 47 guda daya da sauran makamai, wadda a cewarsa, an mika dukkan wadanda aka kama ga hukumomin da abin ya shafa.













































