Majalisar dokokin jihar Kano ta bayyana jin daɗinta kan yadda hukumar kula da tallace-tallace da sanarwa ta jihar Kano KASA ta fara nuna ƙwarewa da ingantaccen aiki cikin watanni uku da kafuwarta.
Majalisar ta yi alkawarin ƙarfafa mata gwiwa ta fuskar kara kasafin kuɗi a shekarar 2026.
Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce shugaban kwamitin kasafin kuɗi Sa’ad Aminu Ungogo ne ya jinjinawa hukumar yayin tattaunawar kasafin shekarar 2026 a zauren majalisar.
Ya bayyana cewa hukumar ta nuna gaskiya da riƙon amana a fannin samar da kuɗaɗen shiga, tare da hasashen cewa za ta samar da Naira biliyan 2.6 a shekarar 2026.
Ungogo ya tabbatar da cewa majalisar za ta ƙara mata tallafin kasafin kuɗi domin ta ci gaba da inganta aikinta da faɗaɗa ayyukanta na dubawa da daidaito a harkokin talla da sanarwa a faɗin jihar.
Haka kuma ya yaba da rawar da hukumar ke takawa wajen dawo da tsari a harkar saka talla, gyaran muhalli, da inganta kyan gani a birnin Kano.
Shugaban kwamitin filaye da tsare-tsaren gari Hafizu Gambo ya ce ingantaccen aikin hukumar, bin ka’idoji, da nuna gaskiya na da matuƙar muhimmanci ga burin sabunta birni da gwamnatin jihar ke yi.
Ya ce matakan da ake ɗauka a KASA sun dace da fasalin tsare-tsare na zamani da ake son cimmawa.
A nasa bangaren, darakta janar na KASA, Kabiru Saidu Dakata, ya gode wa majalisar bisa wannan yabo, tare da tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da aiki bisa ƙwarewa, bin dokoki, da kiyaye ƙa’idoji na duniya wajen kula da tallace-tallace da sanarwa a waje.













































