Kwamitin majalisar dattijai mai kula da asusun gwamnati, ya bai wa kamfanin man fetur na kasa NNPCL wa’adin makonni uku da ya amsa tambayoyin da aka gabatar a cikin rahoton hada-hadar kudi da aka yi a a tsakanin shekarun 2017 zuwa 2023, wanda ya yi zargin cewa ba a gano wasu kudade da suka kai Naira tiriliyan 210 ba.
Kwamitin wanda Sanata Aliyu Wadada mai wakiltar Mazabar Nasarawa ta Yamma ya jagoranta, ya jaddada cewa ba a sace kudaden da ake magana a kai ba, kuma ba a rasa su ba, ba kuma a kai ga tantance su ba har kawo yanzu.
Kwamitin ya ba da wa’adin makonni ukun ne ga babban jami’in kamfanin na NNPC, Injiniya Bayo Ojulari, bayan kwamitin ya amince da uzurinsa na rashin bayyana a gabansa a baya.
Ojulari, bayan neman afuwar kwamitin bisa rashin amsa gayyatar kwamitin a baya sakamakon wasu dalilai, inda kuma ya bukaci karin lokaci domin bibiya tare da amsa tambayoyi 19 da aka gabatar masa, domin kasancewar sun kunshi bayanai na fasaha da mabanbanta ra’ayoyi.
Sai dai, duk da cewa Mista Ojulari, ya bukaci a ba shi makonni hudu, amma kwamitin ya ba shi sati uku, inda ya ce hakan ma zai ishe shi ya shirya rahoton martanin da zai gatar.
Shugaban kwamitin Sanata Wadada ya ce, Naira tiriliyan 210 da ake magana a kai ta kunshi bashin Naira tiriliyan 103 da kuma kadarori na Naira tiriliyan 107, dukkansu ya zama wajibi a yi lissafinsu yadda ya kamata.
Tun da farko, kafin shugaban ya yanke hukuncin, kusan dukkanin mambobin kwamitin sun jaddada muhimmancin batutuwan amma sun nuna kwarin gwiwa cewa GCEO zai ba da haske.
Musamman, Sanata Victor Umeh mai wakiltar mazabar Anambra ta Tsakiya, ya bayyana cewa, “Abu daya da ya kamata a jaddada shi ne bukatar gaskiya. NNPCL na rike da mabudin ci gaban tattalin arzikin Najeriya.”













































