Kotun koli ta ƙasa ta tabbatar da ikon kundin tsarin mulki da shugaban ƙasar Nijeriya ke da shi na ayyana dokar ta baci a kowace jiha domin hana rushewar doka da oda ko shiga cikin rikici mai tsanani.
A hukuncin da aka yanke da rinjayen alkalai shida da ɗaya, kotun ta amince da ikon shugaban ƙasa da ke ƙarƙashin kundin tsarin mulki na 1999 na ayyana dokar ta baci da ɗaukar matakai na musamman domin dawo da zaman lafiya da daidaito.
Kotun ta kuma bayyana cewa a lokacin dokar ta baci, shugaban ƙasa na da ikon dakatar da zaɓaɓɓun jami’an jiha, muddin dakatarwar ta kasance na wani takaitaccen lokaci.
Mai shari’a Mohammed Idris ya bayyana cewa sashe na 305 na kundin tsarin mulki na 1999 ya bai wa shugaban ƙasa ikon ɗaukar matakai na musamman a inda aka ayyana dokar ta baci, tare da nuna cewa kundin tsarin mulkin bai fayyace iyakar irin waɗannan matakai ba, lamarin da ke ba shugaban ƙasa damar yin abin da ya ga ya dace domin dawo da tsari.
Karanta: Majalisar Dattawa na shirin ƙara yawan alƙalan Kotun Ƙoli zuwa 30
Shari’ar ta samo asali ne daga ƙarar da jihohin da PDP ke mulki suka shigar, suna ƙalubalantar ayyana dokar ta baci da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers, inda aka dakatar da zaɓaɓɓun jami’an jihar na tsawon watanni shida.
Masu ƙarar su ne lauyoyin gwamnati na jihohin Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara da Bayelsa, yayin da waɗanda ake ƙara su ne gwamnatin tarayya da Majalisar dokoki ta ƙasa, inda kotun ta yanke cewa ƙarar ba ta nuna sahihin dalilin shari’a da zai sa ta yi amfani da ikon ta na asali ba, saboda haka ta kori ƙarar, duk da haka ta kuma yi la’akari da muhimman batutuwan da aka gabatar tare da watsi da su.
Sai dai a hukuncin da ya bambanta ra’ayi, Mai shari’a Obande Ogbuinya ya amince cewa shugaban ƙasa na da ikon ayyana dokar ta baci, amma ya bayyana cewa wannan iko bai haɗa da dakatar da zaɓaɓɓun jami’an jiha kamar gwamna, mataimakin gwamna da ‘yan majalisar dokokin jiha ba.











































