Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar wa Uba Sani nasara

Uba Sani 750x430
Uba Sani 750x430

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a Abuja ta tabbatar wa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani nasara a zaɓen gwamnan jihar na 2023.

A hukuncin da ta zartar yau Juma’a, kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar PDP, Isa Ashiru ya shigar yana ƙalubalantar nasarar gwamnan na jihar Kaduna.

Tun farko, kotun sauraron ƙorafin zaɓe da ta zauna a Kaduna ta bayyana cewa Isa Ashiru ya gaza cika ƙa’ida game da lokacin shigar da ƙorafinsa na zaɓen gwamna, wanda hakan ya sanya ba za a iya amincewa da ƙorafinsa ba.

Sai dai an samu saɓani tsakanin alƙalan kotun, inda wasu daga cikin suka bayyana cewa akwai buƙatar sake zaɓe a wasu ƙananan hukumomi, in da Ashiru ya shigar da ƙara a kan lokaci.

Sai dai rashin gamsuwa da hukuncin kotun ya sanya dukkanin ƴan takarar biyu garzayawa kotu domin a tabbatar musu da nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here