Kotu ta umarci a sake buɗe makarantar Sakandaren Prime College a Kano

Prime College new 550x430 (1)

Wata kotun majistire da ke zaune a unguwar Gyadi Gyadi a Kano ta bayar da umarnin a bude makarantar sakandare mai zaman kanta, wato Prime College, bayan ta soke umarnin da ya rufe ta.

Alkalin kotun, Hajiya Fauziyya Sheshe, a zaman kotun na ranar Litinin ta ce makarantar ta dawo da aikinta nan take.

Ta bayyana cewa an yi wannan hukunci ne bisa roƙon lauya na gwamnati da kuma ikon kotun na yin adalci.

A baya dai, kotun majistire ta bayar da wani umarni a ranar 16 ga Satumba, bayan ƙarar da hukumar kula da makarantun masu zaman kansu da masu sa-kai a Kano (PVIB) suka shigar, wanda aka ɗaura zuwa ranar 7 ga Oktoba, 2025 domin sauraron ƙarar.

Lauyoyin makarantar sun bayyana cewa sun zo kotun domin ƙalubalantar ingancin wannan umarni na dakatar da makarantar, musamman kan batun karin kuɗin makaranta da iyaye ’yan makaranta suka kai ƙara.

Tun a watan Yuli, 2025, Prime College ta sanar da karin kuɗin makaranta saboda hauhawar farashi da kuma bukatar inganta karatu da kayayyakin makaranta.

Kusan kashi 94 cikin 100 na iyaye sun biya sabon kuɗi, sai dai wasu iyaye ƙalilan ƙasa da 20 suka ƙi amincewa, suna zargin makarantar da cin moriyar jama’a.

PVIB ta shiga tsakani tare da kafa kwamiti na wucin gadi da ya haɗa iyaye da malamai domin tattaunawa.

Duk da cewa yawancin kwamiti ya amince da karin kuɗin, daga bisani hukumar ta ce zaman bai kammalu ba, inda ta bayar da umarnin a janye karin.

Makarantar ta yi ƙoƙarin tattaunawa da hukumar, amma a cewar shugabancin makarantar, an yi mata wariya da ɓata suna.

Daga baya kuma aka fassara umarnin kotu ta hanyar da ta kai ga rufe makarantar baki ɗaya, abin da kotun ta ce ba daidai ba ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here