Kotu ta tabbatar da Machina a matsayin halartaccen dan takarar APC na Yobe ta Arewa

Bashir Machina and Ahmad Lawan
Bashir Machina and Ahmad Lawan

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Damaturu cikin jihar Yobe ta tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halartaccen dan takarar sanata na jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa.

Bashir Sharrif Machina dai tun farko ya ce ba zai sauka ko janyewa kowa takararsa ta majalisar dattijai ba.

Tun bayan kammala zaben fitar da gwani na shugaban kasa a APC dambarwa ta kunno kai kan yiwuwar shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmed Lawan zai rasa takararsa ta sanata bayan ya shafe fiye da shekara ashirin yana wakiltar al’ummarsa a Majalisun Tarayyar ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here