Kotu ta ƙi bayar da belin Farfesa Yusuf Usman

31c296ac 40ee 43fa 9ad1 3a6d9a8d9007.jpg

Babbar kotun Abuja ta yi watsi da buƙatar belin da lauyoyin tsohon shugaban Hukumar Inshoran Lafiya ta Najeriya, Farfesa Usman Yusuf suka nema.

Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa ce dai ta gurfanar da Farfesan bisa zargin bayar da kwangila ba bisa ƙa’ida ba a lokacin da yake jan ragamar hukumar.

Kama tsohon shugaban hukumar Inshorar ya haifar da zazzafar muhawara a ƙasar, inda wasu ke zargin bi-ta-da-ƙulli ne.

Labari mai alaka: Zargin badaƙala: Kotu ta tsare tsohon shugaban NHIS a gidan gyaran hali na Kuje

A yanzu dai kotun ta ɗage sauraron buƙatar belin zuwa ranar 27 ga watan Fabrairun da muke ciki.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here