Katsewar lantarki ya jinkirta zaman majalisar dattawan Najeriya

majalisar dokoki, najeriya, katsewar, wutar lantarki, jinkirta
Wutar lantarki da aka ɗauke a zauren majalisar dokokin Najeriya ya kawo jinkirin fara zaman 'ƴan majalisar dattijai a yau Talata. Sanatocin sun tsaya na wani...

Wutar lantarki da aka ɗauke a zauren majalisar dokokin Najeriya ya kawo jinkirin fara zaman ‘ƴan majalisar dattijai a yau Talata.

Sanatocin sun tsaya na wani lokaci yayin da suke jiran kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Abuja AEDC ya dawo da wutar.

Karin labari: Babban bankin Ghana ya dakatar da lasisin GTB dana First-Bank

Zauren Majlisar ya kasance cikin duhu yayin da wasu tsiraru daga cikin ‘ƴan majalisar suke zaune suna jiran a dawo da wutar.

Sai dai daga baya shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya buɗe zaman bayan dawowar lantarkin.

Karin labari: Jiragen sama biyu sun yi karo a Kenya

Dama dai kamfanin lantarki na AEDC ya koka kan cewa akwai ma’aikatu da hukumomin gwamnati da dama waɗanda yake bi bashi, har ma ya yi barazanar yanke musu lantarki matuƙar ba su biya bashin da ake bin su ba.

Najeriya dai na fama da ƙarancin wutar lantarki, inda ƙasar ta gaza samar da isasshen wutar lantarki da zai wadaci al’umma da masana’antu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here