Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya shiga tsakani a rikicin masana’antu da ke tsakanin Matatar Man Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Mai da Gas ta Ƙasa (PENGASSAN), inda ya yi kira da a yi hattara, a nuna kishin ƙasa, tare da warware matsalar ta hanyar tattaunawa.
Shettima ya ce bai kamata a bari wata ƙungiya ko hukuma ta lalata ƙoƙarin kamfanin matatar man fetur ta Dangote ba, musamman ma saboda rikicin da za a iya magancewa cikin lumana.
A yayin da yake jawabi a taron tattalin arzikin Najeriya karo na 31 da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin, Shettima ya bayyana Aliko Dangote a matsayin hujja da ginshiƙi na tattalin arzikin ƙasa, yana mai cewa dole ne a kare shi da tallafa wa wannan babbar jarin da ya zuba don ci gaban ƙasa.
Labari mai alaƙa: PENGASSAN ta dakatar da yajin aikin da ta fara a kasa baki ɗaya
Ya ce jarin da Dangote ya zuba a cikin wannan matatar man, maimakon saka hannun jari a kamfanonin waje kamar Microsoft ko Amazon, ya nuna irin kishin ƙasar da ke cikin zuciyarsa, don haka ya dace a ɗauki wannan zuba jari a matsayin gadon ƙasa.
Shettima ya roƙi ɓangarorin biyu, ƙungiyar ma’aikata da shugabancin matatar da su bi matsalar cikin natsuwa da fahimtar juna, tare da gujewa duk wani abu da zai kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Ya jaddada cewa wajibi ne gwamnati da ɓangarorin masu zaman kansu su yi aiki tare wajen tabbatar da zaman lafiya a masana’antu domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da ƙarfafa zuba jari.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ƙirƙirar yanayi mai kyau don saka jari da daidaiton masana’antu, yana mai kira ga ‘yan ƙasa da su fifita tattaunawa fiye da takaddama wajen magance matsalolin da ke gaban ƙasar.












































