Kakakin Majalisar Ribas Rt. Hon Edison Ehie ya yi murabus

111
111

Kakakin Majalisar Ribas mai biyayya ga Gwamna Sim Fubara, Rt. Hon Edison Ehie ya yi murabus a matsayin mamba mai wakiltar Ahoada ta Gabas da kuma a matsayin kakakin.

Sanarwar murabus din nasa na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 29 ga watan Disamba 2023 na shekarar da ta gabata, zuwa ga shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu.

“Na rubuta wannan ne don in sanar da ku a hukumance game da murabus dina na radin kaina a matsayin kakakin majalisa kuma dan majalisar dokokin jihar Rivers ta 10 mai wakiltar mazabar Ahoada ta Gabas II daga ranar da wannan wasikar ta fito.”

Wasikar ta kara da cewa “Ina so in jinjinawa abokan aikina da kuma al’ummar mazabata bisa ga damar da suka bani na yin hidima a gare su, kuma ina fatan ci gaba da bayar da iyakacin kokarina na yi wa jihar Ribas hidima.”

A karshe Dan majalisar dai bai bayyana dalilin yin murabus din nasa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here