Jihar Kano da ƙananan hukumomi sun karɓi naira biliyan 348.2 daga asusun FAAC cikin watanni takwas

kano kano 750x430

Jihar Kano ta samu ƙaruwa mai ɗorewa a rabon kuɗaɗen da ta ke karɓa daga Asusun Rabon Kuɗaɗen Ƙasa (FAAC) a shekarar 2025, abin da ke nuna ingantuwar samun kuɗaɗen shiga daga fannin mai da kuma na marasa alaƙa da mai.

Binciken da SolaceBase ta yi bisa bayanan da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa da Ofishin Akanta Janar na Tarayya suka fitar ya nuna cewa gwamnatin jihar da ƙananan hukumomin 44 sun karɓi kuɗaɗe masu ƙaruwa a kowane wata daga Janairu zuwa Agusta 2025 wanda shi ne lokaci mafi kwanciyar hankali a tattalin arziƙin jihar cikin ‘yan shekarun nan.

Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta karɓi jimillar naira biliyan 167 a cikin watanni takwas na farko, inda rabonta ya tashi daga naira biliyan 17.7 a watan Janairu zuwa biliyan 24.9 a watan Agusta hakan ya nuna ƙaruwa da kashi 41 cikin ɗari.

A matakin ƙananan hukumomi kuwa, an samu ci gaba sosai, inda suka karɓi naira biliyan 181.2 gaba ɗaya cikin watanni takwas, da matsakaicin naira biliyan 22.7 a kowane wata wanda ya fi na gwamnatin jiha.

Rabonsu ya tashi daga biliyan 19.5 a watan Janairu zuwa biliyan 26.6 a watan Agusta, abin da ke nuna ƙaruwa da kashi 36 cikin ɗari.

Masana sun danganta wannan ci gaban da daidaita tsarin musayar kuɗi da kuma kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin hukumar tara haraji ta tarayya da Asusun FAAC.

Haka kuma, karuwar kudin mai da harajin cikin gida kamar harajin ƙarin kayayyaki (VAT), harajin kamfanoni da na shigo da kaya sun taimaka wajen ƙara yawan kuɗin rabon ƙasa.

Karanta: NELFUND ta sake buɗe shafin bada launin ɗalibai na shekarar karatu ta 2024/2025

Kwatancen da aka yi ya nuna cewa ƙananan hukumomin Kano sun karɓi fiye da naira biliyan 14.2 sama da gwamnatin jiha a cikin watanni takwas, bisa tsarin FAAC da ke fifita rabon kuɗi zuwa matakin ƙasa.

Wannan na nuna muhimmancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi wajen raya ƙauyuka, ilimi da kiwon lafiya.

Masana tattalin arziƙi sun jaddada cewa idan an gudanar da waɗannan kuɗaɗe yadda ya kamata, za su iya juyar da su zuwa ci gaban zahiri.

Amma sun gargadi cewa hauhawar farashi da tsadar gudanar da gwamnati na iya rage tasirin ribar da ake samu.

Binciken ya kuma nuna cewa wannan cigaba a Kano na cikin alamar farfaɗowar tattalin arziƙin ƙasa gaba ɗaya, domin kusan dukkan jihohi sun fara samun kuɗaɗen FAAC masu yawa tun daga farkon 2025, sakamakon tsadar mai, ingantaccen tari na haraji, da manufofin daidaita tattalin arziƙi na gwamnatin tarayya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here