Ibadan: Damagum, Bala Mohammed, Makinde da wasu sun karɓi tutoci a yayin fara babban taron ƙasa na jam’iyyar PDP

hhpdpsitted 750x430

A birnin Ibadan an fara babban taron ƙasa na jam’iyyar PDP, inda manyan jagororin jam’iyyar suka karɓi tutocin jam’iyyar, tutar Najeriya da tutar taron ƙasa a wani gagarumin taro da ya haɗa dubban wakilai daga faɗin ƙasar.

Shugaban PDP na ƙasa, Umar Ilya Damagum, shi ne ya karɓi tutar jam’iyyar, yayin da shugaban taron, gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri, ya karɓi tutar taron ƙasa da aka tanada domin wannan babban zama.

Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kwamitin gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, ya karɓi tutar Najeriya, inda gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya karɓi tutar jihar Oyo a matsayin mai masaukin baƙi.

Wasu manyan jagororin jam’iyyar da suka karɓi tutoci sun haɗa da shugaban marasa rinjaye a majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro, wanda ya karɓi tutar majalisar Dattawa, da kuma Hon. Fred Agbedi wanda ya karɓi tutar majalisar wakilai.

Labari mai alaƙa: Dalilin da yasa na kai ƙarar PDP Kotu – Lamido

An fara taron ne bayan tantance wakilai sama da 3,000 daga jihohi 36 da birnin tarayya, lamarin da ya zama shiri na ƙarshe kafin gudanar da zaɓen cikin gida domin tabbatar da shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar a matakai daban-daban.

Tun daga ranar Juma’a birnin Ibadan ya cika da magoya bayan jam’iyyar PDP daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka gudanar da liyafar maraba da gwamna Seyi Makinde ya shirya tare da halartar gwamnonin PDP, tsofaffin gwamnoni da shugabannin jam’iyyar.

Liyafar da aka gudanar ta samu halartar manyan jami’ai ciki har da gwamnonin Adamawa, Bauchi, Rivers da Zamfara, tare da tsofaffin gwamnoni Olagunsoye Oyinlola da Ibrahim Dankwambo, a matsayin wani ɓangare na shirin taron ƙasa na PDP da ya gudana a Ibadan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here