Hukumar yaƙi da cin Hanci da rashawa ta Kano ta sanar da sabon shugabanta na riƙo

PCACC NEW 750x400

Hukumar karbar korafi da yaki da cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano PCACC, ta sanar da nadin Barista Zaharaddeen H. Kofar Mata, a matsayin shugabanta riko.

Nadin nasa ya fara aiki nan take, an bayyana shi ne a cikin wata sanarwar hukumar ta fitar yau Litinin mai dauke da sa hannun babban jami’in tsaro na hukumar L. Dauda, a madadin shugaban hukumar.

A cewar sanarwar, matakin ya yi dai-dai da kudurin Hukumar na tabbatar da ci gaba da jagoranci da samar da ayyuka masu inganci a fannin karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa .

Nadin dai yana jiran sabon umarni daga Gwamnan Jihar Kano.

SolaceBase ta ruwaito cewa nadin na zuwa ne bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimigado.

Hukumar ta yi kira ga daukacin Daraktoci da shugabannin sassa da ma’aikata da su bai wa shugaban rikon hadin kai da goyon baya wajen gudanar da ayyukan da ya rataya a wuyansa.

Ana sa ran Zaharaddeen Kofar Mata zai sa ido kan ayyukan hukumar na inganta gaskiya da kula da korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa a fadin jihar.

Sanarwar ta sake jaddada godiyar hukumar na kwazo da kwarewar ma’aikatanta wajen cika aikinta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here