Hukumar tsaron farin kaya ta bukaci ASUU da ta janye yajin aiki.

ASUU strike
ASUU strike

Hukumar tsaro ta farin kaya ta yi kira ga kungiyar malaman jami’o’i da ta janye yajin aikin da take yi.

Daraktan ma’aikatar mai kula da jihar Yobe, Yunusa Abdulkadir ne yayi wannan roko yayin taro zagaye na uku na daraktocin tsaro na jiha a shiyyar Arewa maso Gabas a Damaturu.

Ya ce yajin aikin ba babu shakka ya gurgunta ilimin jami’o’i a kasa inda ya illata harkar tsaro.

Daraktan ya kuma yi kira da a samar da asibitin masu tabin hankali a Yobe domin duba matsalolin da suka biyo bayan tashin hankali da hakan ke haifarwa.

Ya ce rashin yin hakan na iya haifar da munanan raunuka, wadanda zasu haifar da wata barazanar tsaro ga jihar.

A nasa jawabin, shugaban taron, Mista Hassan Abdullahi ya ce taron zai yi nazari kan barazanar tsaro da tattauna hanyoyin da za a bi dan magance matsalar.

Abdullahi wanda shi ne Daraktan DSS na jihar Bauchi ya lissafo matsalolin tsaro a shiyyar da suka hada da ta’addanci, garkuwa da mutane, ‘yan fashi da satar shanu.

Ya yabawa gwamnatin jihar bisa goyon baya da hadin kai ga hukumar DSS da sauran jami’an tsaro.

Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Idi Gubana ya bayyana taron a matsayin wanda ya dace duba da irin kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Gubana ya ba da tabbacin cewa gwamnatin Mai Mala Buni za ta kasance a ko da yaushe tana daidaita kanta da manufofin dukkanin hukumomin tsaro na jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da labarin cewa muhimman abubuwan da suka faru a wajen taron sun hada da bayar da lambar yabo ga sarakunan Fika da Damaturu, Muhammad Ibn Abali da Alhaji Shehu Hashimi bisa rawar da suka taka wajan yakin da ake da ‘yan tada kayar baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here