Hari: Yan ta’adda sun kashe DPO, Soja a Katsina

878E2FF1 56A3 4ECE 823B E8D523B87A53
878E2FF1 56A3 4ECE 823B E8D523B87A53

Wasu ‘yan ta’adda sun kashe jami’in ‘yan sanda wato DPO a wani hari da suka kai garin Jibia da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Jami’in tsaron da aka kashe, A. A. Rano, har zuwa rasuwarsa shi ne jami’in da ke kula da shalkwatar ‘yan sanda da ke Jibia, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana a ranar Laraba.

Ko da yake ba a iya tantance hasarar da ‘yan bindigar suka yi ba, mazauna yankin sun ce an kashe soja guda tare da jikkata wani.

Hukumomin ‘yan sanda da na soji a jihar har yanzu ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

Ba’a iya samun Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah don yin bayani kan batun ba.

Jami’in sojan da ya ji rauni, wanda aka ce jami’in sojan Najeriya ne, an harbe shi a kafarsa.

A cewar mazauna garin na Jibia, ‘yan bindigar sun kai hari garin ne a daren ranar Talata, inda suka rika harbe-harbe akai-akai, lamarin da ya sa jama’a suka firgita.

Sai dai sun yi artabu da wata tawaga ta hadin gwiwa ta jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji.

‘Yan bindigar, a cewarsu, sun gudu daga garin bayan harin amma ba tare da sun yi awon gaba da matar wani dan kasuwa da ba a tantance ba a garin.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane takwas a kauyen Guga da kuma unguwar Galadima da ke karamar hukumar Bakori a jihar.

Channels TV

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here