Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da rabon kayan aikin lafiya da muhimman magunguna da darajarsu ta haura Naira biliyan 23 ga jihohi 36 da kuma Abuja, a wani yunkuri na farfaɗo da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko a ƙarƙashin shirin sabunta fata na gwamnati.
Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya sanar da hakan a Abuja yayin bikin ƙaddamar da shirin, inda ya ce wannan mataki cika alƙawari ne karkashin shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin dawo da martabar cibiyoyin lafiya a matakin farko a matsayin ginshikin tsarin kiwon lafiyar Najeriya.
Ya ce fiye da cibiyoyi 500 za a samar musu da nau’ikan kayan aiki 56 da suka haɗa da injin gwaji, gadon haihuwa, na’urar duban ciki (ultrasound) da kuma injin dumama jarirai.
Haka kuma, nau’ikan magunguna 80, ciki har da na cututtuka, maleriya, hawan jini, da kayan tsarin iyali, za a raba su a faɗin ƙasa.
Karin labari: Likitoci sun fara yajin aikin gargaɗi na kwana biyar
Pate ya bayyana cewa kayan aikin na da darajar fiye da Naira biliyan 9 ne, yayin da magungunan suka kai fiye da Naira biliyan 14, waɗanda aka samar ta hanyar kuɗaɗen gwamnati da tallafin ƙasashen waje.
Ya kuma ce sama da cibiyoyin lafiya a matakin farko 1,295 aka gyara a cikin shekara ɗaya, ciki har da 38 da aka samar musu da hasken rana, tare da horar da ma’aikatan lafiya 69,106 da samar musu da kayan aiki da kayan sawa.
Jihohi kuma suna ƙara ɗaukar sabbin ma’aikata don cike gibi.
Har ila yau, ya nuna cewa shirin MAMII Initiative ya riga ya ɗauki mata masu juna biyu sama da 411,000 a jihohi 21, inda dubban mata suka ci gajiyar tallafin kula da juna biyu, tikitin sufuri da taimakon gaggawa.
Ministan ya gode wa abokan hulɗa kamar UNICEF, Gavi, Global Fund, UNFPA da kuma gidauniyar Bill da Melinda Gates, sannan ya ce dukkan kayan da aka raba za a saka ido ta hanyar tsarin lantarki tare da sa hannun ICPC da hukumomin da suka dace.
Haka kuma, ya sanar da shirye-shiryen yin kamfen ɗin rigakafin cutar Measles-Rubella a watan Oktoba, wanda zai shafi yara sama da miliyan 100 ƙasa da shekaru 14 tare da haɗa shi da kula da abinci mai gina jiki da rigakafin maleriya.














































