Gwamnatin Kano ta gargaɗi matasa kan su guji tada fitina

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi matasa da su daina haddasa rikici tsakanin al’umma ko kuma su fuskanci fushin doka, a daidai lokacin da ta ke kara kaimi wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a daukacin jihar.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa a ranar Talata, wadda Daraktan hulda da jama’a da wayar da kan jama’a na ma’aikatar tsaron cikin gida da ayyuka na musamman, Alhaji Muhammad Dahir Idris, ya sanyawa hannu tare da raba wa manema labarai.

Sanarwar ta ce, an yi wannan gargadin ne a bisa umarnin kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman, Air Vice Marshal Ibrahim Umar mai ritaya, bayan ziyarar da ya kai yankin Kurna Tudun Fulani da ke karamar hukumar Dala, yankin da aka bayyana a matsayin daya daga cikin wuraren da ke fama da matsalar tsaro.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan wasu fusatattun matasa sun kashe Baturen ‘yan sanda na garin Rano CSP Baba Ali, tare da kona ofishin ‘yan sanda da wasu motoci saboda kama wani da ake zargin ya mutu a hannun ‘yan sanda.

“Ziyarar ta biyo bayan bayanan sirri ne da ke nuni da cewa wasu matasa marasa kishin kasa sun addabi mazauna garin, inda suka yi ta lalata dukiya da kuma asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da kisan da aka yi wa Abba Sa’idu Mai Hula a wani rikicin da ya barke a baya-bayan nan,” inji sanarwar.

AVM Umar Mai ritaya ya nuna matukar damuwarsa kan tabarbarewar al’amura tare da jaddada cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na yin kokari wajen ganin an shawo kan matsalar tabarbarewar matasa ta hanyar ba da horon sanin makamar aiki don rage zaman kashe wando da kuma inganta dogaro da kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here