Ƙungiyar kare hakkin ɗan-adam ta Amnesty International reshen Najeriya ta bayyana cewa yawaitar garkuwa da dalibai a makarantu na iya durƙusar da ci gaban ilimi a yankin Arewacin ƙasar.
Sanarwar ta nuna cewa tsoron hare-haren da ake kai wa makarantu na haifar da mummunan tasiri ga tunanin yara, wanda hakan zai hana su sha’awar zuwa makaranta.
A wata hira da gidan talabijin na tashar Channels, Daraktan Amnesty a Najeriya Isa Sanusi ya ce tsananin rashin tsaro ya sa iyaye da dama sun fara sake nazari kan aminci da makomar yaran su wajen halartar makarantu.
Ya bayyana cewa iyalai a yankunan karkara ma na fuskantar matsaloli wajen ci gaba da tura ‘ya’yansu makaranta saboda ƙalubalen tattalin arziƙi, kuma wannan matsalar tsaro na ƙara dagula al’amura.
Sanusi ya kuma bayyana cewa a wasu yankunan karkara yara na taka muhimmiyar rawa a aikin gida, don haka iyaye kan yi tirjuya wajen ba su damar zuwa makaranta, lamarin da yanzu zai ƙara rikicewa saboda tashin hankalin tsaro.
Ya gargadi cewa idan wannan hali ya ci gaba, zai sanya wannan ƙarni gaba ɗaya ya rasa damar samun ilimi, musamman a Arewa, inda adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya riga ya kai sama da miliyan goma sha biyu.
A kwanakin nan an sake samun tashin gwauron zabi na hare-hare a cibiyoyin ilimi, lamarin da ya sa gwamnatocin jihohi da dama suka rufe makarantu na ɗan lokaci, ciki har da harin da aka kai makarantar ƴan Mata a Maga da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, da kuma harin da aka kai makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri a Jihar Neja, inda aka yi garkuwa da ɗalibai da malamai da dama.













































