Fashewar gas ɗin Kano: Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa mutane tara

Kano Explosion 678x381 1
Kano Explosion 678x381 1

Gwamnatin tarayya ta ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon fashewar iskar gas da ta afku a jihar Kano yau Talata ya karu zuwa mutane tara.

Hukumar bada agajin gaggawa ta tarayya ce ta bayyana haka lokacin da babban daraktan hukumar na ƙasa Mustapha Habib Ahmed, ya je wurin da lamarin ya faru.

Ko da yake a baya rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da mutuwar mutane hudu inda ta ce, fashewar iskar gas ce ba bam ba ne.

“Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 9 daga ɓaraguzan ginin da ya ruguje a gefen wata makarantar firamare sakamakon fashewar wani bututun iskar gas a hanyar Aba dake unguwar Sabon Gari a jihar Kano.

“DG @nemanigeria Mustapha Habib Ahmed yana wurin da lamarin ya faru kuma ya haɗa aikin ceto, A halin yanzu NEMA tana gudanar da ayyukan ceto tare da sauran hukumomi,” kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na twitter.

Solacebase ta ruwaito cewa lamarin da ya faru da sanyin safiya inda ya haifar da tashin hankali a cikin birnin Kano yayin da iyayen suka garzaya zuwa makarantu domin kwashe ƴaƴansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here