Hukumar kula da Filayen Jiragen sama ta ƙasa FAAN ta bayyana cewa za a rufe hanyar shiga tsakanin filin jirgin sama na cikin gida Murtala Muhammed Terminal 2 da kuma na ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed a Legas na ɗan lokaci a ranar Asabar.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Juma’a, hukumar ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa rundunar sojin sama ta Najeriya damar gudanar da gudu na shekara-shekara mai tazarar kilomita goma.
FAAN ta bayyana cewa za a fara wannan motsa jiki da misalin ƙarfe shida na safe, kuma jami’an tsaro za su kasance a dukkan sassan hanyar domin sarrafa zirga-zirga da tabbatar da tsaro ga jama’a.
Hukumar ta tabbatar da cewa wannan rufewar ba za ta shafi ayyukan filin jirgin sama ba, domin dukkan tashi da saukar jirage za su ci gaba kamar yadda aka tsara
. Ta kuma bayyana cewa za a buɗe hanyoyin gaba ɗaya bayan kammala atisayen.
FAAN ta shawarci fasinjoji da masu amfani da filin jirgin sama su tsara tafiyoyinsu tun da wuri, domin ana iya samun dan jinkiri a zirga-zirgar ababen hawa a yankin yayin atisayen.
Hukumar ta nemi afuwa bisa duk wata damuwa da hakan zai iya haifarwa, tare da roƙon jama’a da su ba da haɗin kai da fahimta yayin wannan ɗan gajeren lokaci na rufe hanya.













































