Dalilin da ya sa muka tsawaita yajin aikin da makonni 8- ASUU

6B37873D 0E2A 4516 97A7 D230C557E337
6B37873D 0E2A 4516 97A7 D230C557E337

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce za ta ci gaba da yajin aikin na tsawon makwanni takwas domin baiwa Gwamnatin Tarayya damar magance matsalolin da ake fuskanta a zahiri.

Shugaban ASUU, Mista Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a karshen taron gaggawa na majalisar zartarwa ta kasa ranar Litinin a Abuja.

Osodeke ya ce za a fara yajin aikin ne da karfe 12:01 na safe a ranar Litinin, 14 ga watan Maris.

Solacebase ta bayar da rahoton cewa kungiyar ta shiga yajin aikin gargadi a fadin kasar domin matsawa mambobinta bukatun daga watan Fabrairu 14.

Bukatun malaman sun hada da bayar da kudade na Farfado da Jami’o’in Jama’a, bayar da Lamuni na Ilimi, tsarin biyan malaman Jami’a na (UTAS) da basussukan ci gaba.

A cewar Osodeke,  shugabannin kungiyar sun gudanar da wasu tarurrukan tattaunawa da jami’an gwamnati a cikin makonni hudu da suka wuce yajin aikin.

“Duk da haka, kungiyar ta ji takaicin yadda gwamnati ta ki kula da al’amuran  cikin gaggawa har aka shafe makonni 4.

“kungiyar ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin na tsawon makwanni takwas domin baiwa gwamnati karin lokaci don magance duk wasu batutuwan a zahiri domin gwamnati ta dawo cikin gaggawa.” Inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here