Daga Karshe dai Jonathan ya amince da tayin Fom din takarar da wata Kungiya ta saya masa

Jonah jonah 1 678x381 1
Jonah jonah 1 678x381 1

Awwanni kalilan da barranta kansa da ga wani yunkuri da wasu kungiyoyi sukai na sanya shi gaba a matsayin dan takararsu a zaben shugaban kasa a shekarar 2023, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya amince da bukatar neman kujerar ta lamba daya a kasa.

A ranar litinin din da ta gabata ne Jonathan ya yi watsi da fom din takarar shugabancin kasa wadda wata kungiyar Fulani ta saya masa, inda suka bayyana shi a matsayin shugaban da ya kula da Fulani da kuma almajirai.

Najeriya dai ta dau harama dan gane da zaben na shekarar badi, inda dandazon mutane zasu fito domin kada kuri’un su na raba gaddamar ‘yan takara da suka fito daga mabanbantan jam’iyyu ciki kuwa hadar da jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

A baya dai an ambato Jonathan, yana bayyana cewa cin fuska ne mutane su saya masa fom ba tare da amincewar sa ba, sai dai yanzu tsohon shugaban kasar ya amince da tayin.

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN cewa, hakika tsohon shugaban kasar ya koma jam’iyyar APC ne a hukumance, bayan da ya yi rajista a Mazabarsa ta Otuoke dake jihar Bayelsa.

Majiyar ta kuma bayyana cewa a ranar Alhamis din nan ce ake sa ran Jonathan din zai mika fom din takarar da kungiyoyin Fulani da makiyaya suka saya masa, bayan cikewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here