Fafaroma Francis ya mutu ne a ranar Litinin, yana da shekaru 88, kwana guda bayan da ya yi wani kyakkyawan fata a dandalin Saint Peter a ranar Lahadin Easter, kamar yadda fadar Vatican ta bayyana.
“Ya ku ‘yan’uwa maza da mata, cikin matukar bakin ciki dole ne in sanar da mutuwar Ubanmu Mai Tsarki Francis,” in ji Cardinal Kevin Farrell a cikin wata sanarwa da fadar Vatican ta buga a dandalin Telegram.
“A safiyar yau da karfe 7:35 na safe (0535 GMT) Bishop na Rome, Francis, ya koma gidan Uba.
“Dukan rayuwarsa ya sadaukar da shi ga hidimar Ubangiji da cocinsa.”
Mutuwar Francis ta zo kwana guda bayan da ya farantawa ɗimbin masu ibada a fadar Vatican ranar Lahadin da ta gabata tare da bayyana a baranda a Basilica na Saint Peter’s Basilica duk da cewa yana fama da rashin lafiya.
Francis ya auna mutuwa sau biyu a farkon wannan shekara yayin da yake fama da ciwon huhu.
Ya kwashe kwanaki 38 a asibiti kafin a sallame shi a ranar 23 ga Maris.
A ranar Lahadin da ta gabata ya yi wa taron jama’a a dandalin Saint Peter fatan “Barka da Esater” yayin da yake daga hannu kuma a cikin al’adun gargajiya na “Urbi et Orbi” (“Ga birni da Duniya”) ya yi kira da a zurfafa tunani da hakuri.