Da ɗumi-ɗumi: Ministan kimiyya da fasaha ya sauka daga muƙamin sa

Bola Tinubu Tinubu Kano 750x430

Ministan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya sauka daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta nuna cewa Nnaji ya miƙa takardar ajiye aikinsa ga shugaban ƙasa, bayan ya yi shekaru kaɗan yana rike da kujerar minista a fannin kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha.

Ana zargin murabus ɗin nasa na iya zama wani ɓangare na sauye-sauyen da ake sa ran gwamnatin Tinubu za ta yi a cikin majalisar ministoci don ƙara haɓaka aikin gwamnati.

Tun bayan da aka nada shi a shekarar 2023, Nnaji ya jagoranci wasu muhimman shirye-shirye na bunkasa fasaha da kirkire-kirkire a Najeriya, musamman wajen karfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.

Shugaban ƙasa dai bai nada wanda zai maye gurbin Nnaji ba a halin yanzu, yayin da ake sa ran za a sanar da sabon minista a nan gaba kadan.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here