Chanjin kudi: An sanya POS a Gidan makoki saboda daina karban tsaffin kudi

WhatsApp Image 2023 02 20 at 3.08.39 PM
WhatsApp Image 2023 02 20 at 3.08.39 PM

A gabar da gwamnatin tarayya karkashin bqbban bankin kasa CBN ya bada umarnin daina amfani da tsaffin kudi, 500 da 1000, ayanzu haka an sami wasu magidanta dake zaman makoki sanya na’urar cirar kudi POS dan karban sadaka da tallafi da gudummawa ga iyalan su.

Yayin jana’izar a jihar Anambra, ‘yan uwa sun bayyana karara cewa ba za su karbi tsofaffin takardun naira ba, kuma wadanda basu da sabon kudi za su iya biya da katin ATM din su ta hanyar amfani da PoS.

Rahotanni sun kuma ce, iyalan marigayin sun ba da bayanan asusun ajiyar bankjn su ga waɗanda suka fi son ba da gudummawa ta hanyar tura kudin ta hanyar taransifar banki.

Hakan na zuwa ne a yayin da aka haramtawa tsofaffin takardun kudi na N500, N1000 zagayawa, sannan kuma sabbin takardun kudin suka yi karanci.

Jamaa da dama na kallon wannan mataki a matsayin wani sabon salo dan magance tirka tirkar karancin sabbin kudade a hannun jamaa.

Rahotanni sun nuna yadda mutane sukai cirko cirko tareda gutsuri tsomar kan sanya naurar cirar kudin agidan makokin

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here