Boko Haram ta fara ne a lokacin mulkinka – fadar shugaban ƙasa ta maida martani ga Obasanjo

President Bola Tinubu with former President Olusegun Obasanjo 730x430

Gwamnatin Tarayyar ta soki tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da sauran masu suka game da kokarin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na yaki da ta’addanci a Najeriya, tana masu cewa suna kokarin tauye ci gaban da ake samu wajen shawo kan matsalar tsaro.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da sadarwa ta jama’a, Sunday Dare, ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa maganganun Obasanjo da wasu shugabannin siyasa suna nuna cewa gwamnatin yanzu ba ta iya kare ‘yan ƙasa, alhali kuwa ba su yi la’akari da gaskiyar yawaitar barazanar ta’addanci a ƙasar ba.

Sanarwar ta ce tsohon shugaban ƙasa da wasu manyan ‘yan adawa sun yi suka kan karuwar hare-hare a sassan ƙasar, suna zargin cewa gwamnati tana amfani da dabarun sulhu maimakon amfani da karfi wajen magance matsalolin tsaro.

A wani taro da aka gudanar a Jos jihar Filato, Obasanjo ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yawaitar rashin tsaro, tare da cewa ‘yan Najeriya na da damar neman taimakon ƙasashen waje idan gwamnati ta kasa kare su, abin da Dare ya bayyana a matsayin rashin tunani da rashin adalci ga hakikanin tarihin matsalar Boko haram.

Fadar shugaban ƙasa ta ce Boko haram ta samo asali tun a zamanin mulkin farar hula na Obasanjo, lokacin da ƙungiyar ta yi shela ta tara mabiyanta, ta kafa sansanoni, kuma gwamnati ba ta ɗauki matakin da ya dace ba domin kakkabe su tun farkon fara tashin hankalinsu ba.

Dare ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana tunkarar barazanar ta’addanci ta hanyoyi da dama, ciki har da matsin lamba na soji, bincike ta hanyar leƙen asiri, dawo da gudanar da mulki a yankunan da ake fama da rikice-rikice, da kuma shirin kawar da tsattsauran ra’ayi a al’umma.

Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa irin kalaman tsofaffin shugabanni kan iya ƙarfafa gwiwar ‘yan ta’adda, la’akari cewa abin da ake bukata shi ne haɗin kai daga dukkan ‘yan ƙasa domin mara baya ga gwamnati wajen tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here