“Ana amfani da wasu jiragen sama wajen aikata manyan laifuka a Najeriya” – Keyamo

Jiragen, sama, amfani, wasu, wajen, aikata, manyan, laifuka, Najeriya, Keyamo
Ministan Sufurin Jiragen Sama da Cigaban Jiragen Sama Festus Keyamo, ya ce ana amfani da wasu jiragen sama masu zaman kansu da ke aiki a Najeriya wajen...

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Cigaban Jiragen Sama Festus Keyamo, ya ce ana amfani da wasu jiragen sama masu zaman kansu da ke aiki a Najeriya wajen safarar kudade da safarar muggan kwayoyi da sauran ayyukan da suka sabawa doka.

Keyamo ya bayyana hakan ne a ma’aikatar sufurin jiragen sama da ke Abuja ranar Alhamis, a lokacin da ya kaddamar da kwamitin da ke kula da harkokin sufurin jiragen sama na Ministoci domin tantance ayyukan hayar da aka saba yi a kasar.

Karin labari: PSC / FCCPC: Shugaba Tinubu ya aike da sunayen mutane 3 ga Majalisar Dattawa

Duk da cewa ministan bai ambaci sunayen kamfanonin jiragen ba, amma ya tabbatar da cewa wadannan haramtattun ayyuka sun sa bangaren ya yi asarar biliyoyin daloli tare da haifar da matsalar tsaro sosai.

Ministan ya ci gaba da cewa wasu daga cikin wadanda ke aikata wannan aika-aikar akwai wadanda suka samu lasisin zirga-zirgar jiragen sama ba na kasuwanci ba amma sun sabawa yarjejeniyar lasisin.

Karin labari: Yanzu-yanzu: NELFUND ta amince da bayar da lamunin ɗalibai

Da yake jawabi ga mambobin kwamitin, Keyamo ya umarci da su dauki lissafin duk ma’aikatan jiragen da ba na kasuwanci ba, su binciki duk wasu lasisin kwararru da tantance sahihancinsu tare da bayar da shawarar daukar matakan ladabtarwa kan kamfanonin jiragen sama da aka samu da laifi.

Kwamitin mai mutane takwas yana karkashin jagorancin babban jami’in kula da ‘yan kwangilar Aero, Ado Sanusi, kuma ana sa ran kwamitin zai mika rahoton duk sakamakon binciken ga ministan nan da watanni uku masu zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here