An sanya wa’adin rufe rajistar aikin Hajji a Kamaru

Kamaru, rufe, rajistar, hajji, aikin
Hukumomi a jamhuriyyar Kamaru sun sanya ranar 15 ga watan Maris, 2024, a matsayin ranar da za'a rufe rajistar maniyyata aikin hajjin bana. A cikin sanarwar...

Hukumomi a jamhuriyyar Kamaru sun sanya ranar 15 ga watan Maris, 2024, a matsayin ranar da za’a rufe rajistar maniyyata aikin hajjin bana.

A cikin sanarwar da ministan cikin gida kuma shugaban hukumar aikin hajji na Kamaru, Paul Atanga Nji ya fitar, ya ce Saudi Arabia ta warewa ƙasar kujeru 10,000.

Kuma idan aka cike dukannin kujerun, za’a rufe rajistar gabannin cikar wa’adin.

Karin labari: Jiragen sama biyu sun yi karo a Kenya

Sai dai gabannin an bayyana sabon farashin zuwa hajjin, wanda ya ƙaru a bana da CFA 33,100, shugabannin tawagogin maniyyatan sun fara kira da su yi rajista domin kaucewa cunkoson karshen lokaci.

A bana hukumomin Saudiyya sun sauya tsarin bayar da takardun bizar aikin hajjin, inda suka ce zasu rufe da wuri.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here