Babban jami’in da ke tattara sakamakon zaɓe a Hukumar Zabe ta Abuja, Farfesa Sani Saka, ya sanar da soke sakamakon zaɓen ‘yan majalisar dattawa na babban birnin tarayya Abuja.
Da yake sanar da soke zaɓen a cibiyar tattara sakamakon zaɓen a babban birnin tarayya Abuja ranar Litinin, ya ce an soke sakamakon zaben ne saboda an kaɗa ƙuri’a fiye da adadin waɗanda ke rijista.
Ya ce, “Mun yi watsi da sakamakon Abaji ne saboda kuri’un da aka kaɗa sun zarce yawan waɗanda aka tantance.
A cikin kananan hukumomi shida da ke babban birnin tarayya Abuja, an ci gaba da tattara sakamakon zaɓen karamar hukumar Bwari ne kawai har zuwa lokacin rubuta wannan labari.












































