Kungiyar farar hula ta SINET ta roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati Mista Abdulrashid Bawa da su duba yadda Shugaban Hukumar Shiyya ta Ilorin Michael Nzekwe ke yi. Lamarin da ya sanya yake damfarar masu saka hannun jari a jihar Kwara sake-ba-kaidi.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas ta hannun kodinetan ta na kasa, Mista Oluseyi Adedoyin, Kungiyar ta bayyana bacin ranta kan yadda hukumar EFCC ke kama masu harkar hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar Kwara.
SINET ta kuma danganta ci gaba da kame masu saka hannun jari da ba su ji ba ba su gani ba na gida da kuma na kasashen waje da wani aiki da ya yi daidai da yin amfani da mulki, da gangan a yunkurin talauta jihar ta hanyar korar masu zuba jari daga jihar yana mai jaddada cewa, “Mr. Nzekwe na daya daga cikin masu rura wutar rikici a jihar
A bayanan da hukumar ta tattaro a watan Fabrairu, 2014 ta korar su ba bisa kaida ba wanda hakan babban laifi ne.
Ya nanata kudirin korar sa ne a kotun masana’antu ta kasa, inda aka bayar da umarnin mayar da shi bakin aiki a watan Oktoba, 2015, a cewar alkalin, ya kamata a gurfanar da shi a gaban shari’a tare da hukunta shi kan laifukan ladabtarwa kamar yadda doka ta tanada.
Ya kuma jaddada cewa, “Dokoki ne ke jagorantar ’yan Najeriya ba tunanin kowa ba. Adan haka Mista Nzekwe kamata yayi ya mutunta doka kuma ya daina muzgunawa marasa laifi.











































