Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar.
Nasiru Gawuna ya doke abokin karawarsa Sha’aban Ibrahim Sharada a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a daren jiya Alhamis a filin wasa na Sani Abacha.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen shugaban kwamitin zaben fidda gwanin na ɗan takarar gwamna sanata Tijjani Yahaya Kaura, ya ce Gawuna ya samu ƙuri’u 2,289 yayin da Sha’aban Sharada ya samu kuri’u 30.
Kaura ya ce, jimillar wakilai 2,420 suka halarci aikin zaɓen inda aka kaɗa ƙuri’u 2,339 yayin da guda 20 daga ciki suka lalace.
Wakilan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, ƴan Sanda da Jami’an tsaron farin kaya suka jagoranci zaɓen fidda gwanin.












































