Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet, ta yi hasashen samun hadari da rana daga ranar Larabar makon nan zuwa Juma’a.
Rahoton hasashen yanayin na NiMet da aka fitar ranar Talata a birnin tarayya Abuja, ya yi hasashen yanayi mai hadari tare da tazarar hasken rana a daukacin yankin Arewacin Najeriya a ranar Laraba.
Haka kuma rahoton ya yi hasashen yiwuwar samun Cida da rana da marece.
“Yankin Arewa ta tsakiya ya kasance cikin gajimare tare da hasashen tsawa a cikin yankunan Taraba, Benue, Nasarawa da kuma babban birnin tarayya da safe.
“A washegari, ana hasashen za a yi Cida a sassan jihohin Filato, Kwara, Nasarawa, Neja da Kogi da kuma birnin tarayya.
“Biranen ciki da na bakin teku na Kudu ana sa ran za su kasance cikin gajimare tare da yiwuwar samun Cida a wani bangare na Ebonyi, Abia, Imo, Enugu, Lagos, Delta, Akwa Ibom, Rivers, Cross River da Bayelsa da safe,” a cewar hukumar.
Haka dai, a cewarta, ana sa ran za a yi Cida a duk faɗin yankin nan gaba kadan.
Hukumar ta yi hasashen samun Cida ranar Alhamis tare da tazarar hasken rana a ɗaukacin yankin Arewaci tare da yiwuwar yin Cida da tsakar rana da kuma yammaci.
Haka kuma hukumar ta yi hasashe cewa yankin Arewa ta tsakiya zai kasance cikin gajimare tare da yiwuwar samun Cida a wasu sassan Neja da Plateau da Kogi da kuma babban birnin tarayya da rana da yammaci.
“ Jihohin da ke cikin kasa da na gaɓar tekun yankin kudancin Najeriya za su kasance cikin yanayin gajimare tare da yiwuwar samun tsawa a sassan jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ribas da Bayelsa.
“A cikin wannan rana, ana sa ran za a yi Cida a yankunan jihohin Ogun, Osun, Oyo, Ekiti, Anambra Abia, Enugu, Ondo, Edo, Rivers, Cross River, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta da kuma jihar Legas,” in ji ta.
Ka zalika NiMet ta yi hasashen yanayin rana a ranar Juma’a tare da gajimare a yankin Arewa.
A cewarta, ana sa ran yankin Arewa ta tsakiya zai kasance cikin yanayin rana tare da gajimare.
“Akwai yiwuwa yanayin hazo tare da hasken rana zai mamaye biranen yankunan da ke gaɓar teku.
“Ana sa ran za a yi Cida a wasu cikin yankunan Ebonyi, Enugu, Imo, Osun, Edo, Ekiti, Ondo, Ogun, Bayelsa, Rivers, Cross River Delta, Lagos da Akwa Ibom a lokacin rana da yamma,” a cewar hukumar.












































