Gamayyar jami’an soji masu ritaya, ‘yan sanda, ma’aikatan farin kaya (DSS), jami’an tsaron da ba soju ba da manyan ma’aikatan gwamnati a Kano sun kafa kungiya da nufin karfafa zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
Kungiyar, wacce ke aiki karƙashin sunan (Retired Military, Police, DSS, Paramilitary and Senior Civil Servants Kano for UM), ta ce shirin ba na siyasa ba ne kuma an mayar da hankali ne kan tallafawa kokarin kare rayuka da dukiyar al’umma ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, shugaban kungiyar, Kanar Yusuf Maitama Aminu (mai ritaya) ya ce mambobin kungiyar, duk da sun yi ritaya daga aiki, har yanzu suna da kudurin tallafawa aikin hukumomin tsaro a jihar.
A cewarsa, kungiyar ta yi rajista bisa doka kuma ta fara ziyar wayar da kai zuwa manyan cibiyoyin tsaro, ciki har da Sojojin Najeriya, ‘Yan Sandan Najeriya, Rundunar Tsaron ta Farin Kaya, Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) da Hukumar Tsaro da Kare Farar Hula ta Kasa (NSCDC). Haka kuma suna da shirin fadadawa zuwa bangarorin gargajiya da na addini.
SolaceBase rawaito cewa kungiyar ta bayyana kalubalen zamantakewa irin su fashi da makami, shaye-shaye, ‘yan gudun hijira, yaran dake gararamba a titi da tashin hankalin matasa a matsayin manyan matsalolin da ke bukatar a yi gaggawa wajen magance su. Ta ce magance wadannan matsalolin na daga cikin manyan abubuwan da take bai wa fifiko wajen tallafawa gwamnati da al’umma wajen inganta tsaro.
Kungiyar ta kuma yi kira ga masu hannu da shuni, kungiyoyin al’umma, kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin gwamnati da su hada kai domin cimma abin da ta kira “Better Kano” ta hanyar hadin gwiwa wajen yaki da laifuka da barna a cikin al’umma.
Shugaban ya tabbatar wa al’umma cewa mambobin kungiyar za su yi amfani da gogewarsu da sanayyar da suke da ita a lokacin aiki domin daukar matakan rigakafi da martani domin inganta tsaron jama’a da walwalar zamantakewa a fadin jihar.












































