Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Kano mai sanya ido kan aikin gona da albarkatun kasa, ya yi kiran da a dauki matakin gaggawa kan barkewar cutar (Tuta Absoluta) da ke lalata gonakin tumatur a jihar.
Shugaban Kwamitin, Alhaji Ahmed Ibrahim (Karaye), ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin gabatar da rahoton kwamitin kan barkewar cutar a gaban majalisa.
Ibrahim ya ce an ba kwamitin aiki don yin nazari kan yaduwar cutar biyo bayan kudirin gaggawa da Ali Lawan Kiyawa (Bagwai/Shanono) ya gabatar kan yaduwar Tuta Absoluta, wadda ake kira da Sharon a mazabarsa.
Ya ce binciken ya nuna cewa cutar ta bazu zuwa manyan yankunan da ake noman tumatur, ciki har da Bagwai, Shanono, Rogo, Tofa, Bunkure, Kura, Garun Malam, Rano, Kibiya, da wasu sassa na kananan hukumomin Tudun Wada da Dawakin Kudu.
A cewar Ibrahim, Tuta Absoluta na kai hari ga tumatur a kowane mataki na girma, tana lalata ganye, kara, furanni, da ‘ya’yan itatuwa, wanda hakan ke haifar da asar amfanin gona mai yawa idan ba a dauki mataki yadda ya kamata ba.
“Barkewar cutar zata haifar da mummunan sakamako, ba ga manoma kadai ba har ma ga jihar da kasa baki daya, tana haifar da karancin tumatur da tashin farashi a fadin kasar,” in ji shi.
Shugaban kwamitin ya roki majalisa da ta umarci gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki da su dauki mataki cikin gaggawa domin dakile cutar.
A cewarsa, barkewar cutar na faruwa duk shekara, musamman a lokacin bazara. Don magance hakan, kwamitin ya ba da shawarwari kamar: samar da kayayyaki cikin gaggawa ga Hukumar Raya Aikin Gona da Karkara ta Jihar Kano, KNARDA, ciki har da magungunan kashe kwari da aka amince da su, tarkon pheromone, kayayyakin feshi, kayan kariya, da sauran kayan aiki domin sarrafa barkewar cutar da hana yaduwa.












































