Gwamnatin Jihar Kano ta kara kaimi wajen dawo da cikakken samar da ruwa a fadin jihar, biyo bayan bayar da kwangilar gyaran matatun ruwan Challawa da Tamburawa a makon da ya gabata. Wani mataki da ake sa ran zai dawo da kashi 83 cikin 100 na rarraba ruwa ga manyan biranen jihar Kano.
Wannan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa na Rikon Kwarya, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, bayan ziyar gani da ido da ya kai matatar ruwan Watari.
SolaceBase ta ruwaito cewa wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da Kano ke fuskantar matsalar karancin ruwa da ta dade, wanda galibi ke da nasaba da dadewar da kayayyakin aiki, barnar ambaliya, da shekarun da aka dauka ba a aiki da manyan wuraren samar da ruwa.
A kwanaki baya, gwamnatin jihar ta amince kuma ta sanya hannu kan kwangilolin da su ka kai darajar biliyoyin naira da kamfanonin CGC Nigeria Ltd da CCECC Nigeria Ltd domin gyaran matatun Tamburawa da Challawa, wadanda a yanzu ke aiki kasa da yadda ya kamata. Alal misali, Tamburawa na aiki ne kusan kashi 27 cikin 100 saboda barnar ambaliya, yayin da Challawa ke samar da kasa da kashi 30 cikin 100 na karfinta na asali.
A yayin ziyar, Dr. Hashim ya ce duba tashar Watari ya yi daidai da kudurin Gwamna Abba Kabir Yusuf na tabbatar da an dawo da manyan matatun ruwa guda uku zuwa matakin aiki mafi kyau.
Ya bayyana cewa Watari na taka muhimmiyar rawa a bangaren samar da ruwa na biranen Kano, inda take samar da sauran kashi 17 cikin 100 na bukatar ruwan birnin cikin radius na kilomita 50.
Ya kara da cewa tashar, wadda kuma ke hidima wa kananan hukumomin Bagwai, Bichi da Tsanyawa, tana da karfin samar da lita miliyan 70 a kowace rana amma a yanzu tana aiki ne kusan kashi 50 cikin 100 na karfinta.
“Binciken fasaha da muka yi ya tabbatar da cewa duk da tashar tana da karfin samar da lita miliyan 75 a kowace rana, a yanzu tana aiki ne kusan rabin hakan, muna mai da hankali kan cike wannan gibin domin mayar da tashar zuwa cikakken karfin aiki,” in ji shi.
Dr. Hashim ya kuma tabbatar wa al’umma cewa gwamnatin ta tsaya tsayin daka wajen kawo karshen karancin ruwa ta hanyar samar da mafita mai dorewa da ta dade.
“Mun kuduri aniyar tabbatar da samun isasshen ruwan sha mai tsafta ga duk mazauna cikin birni da al’ummomin da ke kewaye,” in ji shi.
Ana sa ran gyaran manyan tashoshi guda uku Tamburawa, Challawa, da Watari zai dawo da karfin samar da ruwa ga Kano baki daya zuwa kusan lita miliyan 370 a kowace rana, lamarin da zai inganta samuwar ruwa ga miliyoyin mazauna.










































