Ƙungiyar Likitoci ta fara yajin aiki a fadin ƙasa

Doctors NARD 750x430

Kungiyar kwararrun likitoci ta ƙasa ta fara yajin aikin sai Bana-ta-gani tun daga ƙarfe goma sha biyu na dare a ranar Asabar, ɗaya ga watan Nuwamba, shekara ta 2025.

An shirya wannan yajin aiki ne domin tilasta wa gwamnatin tarayya ta cika jerin bukatu goma sha tara da kungiyar ta bayyana a matsayin mafi ƙarancin abin da take buƙata, bayan ta kasa aiwatar da su tsawon lokaci.

Wannan mataki zai shafi ayyukan jinya a asibitocin gwamnati a fadin ƙasar.

Shugaban kungiyar, Dakta Muhammad Suleiman, ya bayyana cewa an yanke wannan shawara ne bayan ganawar gaggawa ta majalisar zartarwa ta ƙasa ta kungiyar a makon da ya gabata, inda aka tattauna matsalolin da ke addabar ma’aikatan lafiya da batutuwan albashi da alawus.

Ya ce gwamnatin tarayya na bin ma’aikatan lafiya sama da naira biliyan 38 na bashin alawus da sauran hakkoki, yayin da wasu asibitoci ke ci gaba da aiki cikin matsin tattalin arziki da ƙarancin ma’aikata.

Bukatun kungiyar sun haɗa da biyan bashin kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari na tsarin albashin likitoci (CONMESS), biyan alawus na kayan aiki na shekarar 2024, da kuma dawo da likitoci biyar da aka kora daga asibitin koyarwa na tarayya da ke Lokoja tare da cikakken biyan hakkokinsu.

Haka kuma kungiyar na neman a inganta yanayin aiki domin ya dace da ƙa’idodin ƙasashen duniya, bayar da damar ɗaukar sabbin ma’aikata a asibitoci, biyan alawus ga likitoci na musamman da daidaita matsayi na albashi.

Kungiyar ta kuma bukaci a kammala aikin kwamitin tattaunawa kan sake duba tsarin albashi, tabbatar da daidaiton albashi tsakanin ma’aikatan lafiya da sauran jami’an gwamnati, da kuma aiwatar da tsarin fansho na musamman ga likitoci.

Haka nan, kungiyar likitoci kwararru ta babban birnin tarayya (ARD-FCTA) ta kuma sanar da fara nata yajin aiki a rana ɗaya saboda matsalolin albashi da rashin daukar sabbin ma’aikata a asibitocin Abuja, inda ta bayyana cewa ba za ta janye ba har sai an biya duk bukatunta na musamman.

Ana sa ran wannan yajin aiki zai haifar da cikas mai tsanani ga harkokin lafiya a ƙasar, la’akari da cewa likitocin su ne ginshiƙin ayyukan jinya a asibitocin gwamnati a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here