Karamar Hukumar Yauri a Jihar Kebbi ta sanya dokar hana fita daga ƙarfe 10 na dare zuwa ƙarfe 7 na safe bayan rikicin da ya barke tsakanin matasa masu hakar zinare a garin Garin Katta.
Rikicin ya samo asali ne daga rashin jituwa tsakanin masu haƙar ma’adinai, wanda ya jawo asarar rayuka tare da lalata dukiya.
Sai dai har yanzu ba a bayyana adadin waɗanda suka mutu ba.
Shaidu sun bayyana cewa rikicin ya fara ne a ranar Asabar da ta gabata lokacin da wasu masu hakar zinare suka kai wa wani hari har suka kashe shi.
Da rana ta gaba, dangin mamacin sun ɗauki fansa inda suka kai hari kan masu hakar ma’adinai.
Bisa ga rahotanni, masu hakar zinaren sun shiga garin suna cin zarafi, suna lalata shaguna tare da ƙona babura ba tare da bambancewa ba.
Wannan ya sa shugaban karamar hukumar, Abubakar Shuaibu, ya sanar da dokar hana fita bayan ya tuntuɓi kwamandan ‘yan sanda da hukumar tsaro da DSS domin dakile tashin hankali.
An binne gawar mamacin bisa tsarin Musulunci, inda shugaban karamar hukumar ya ce sun nemi a bayyana sunayen waɗanda suka aikata kisan, amma wasu daga cikin jama’a suka hana hakan.
Ya ce saboda haka ya kira sakataren gwamnatin jiha, amma bai same shi ba, don haka ya nemi taimakon sojoji domin dawo da zaman lafiya.
Shuaibu ya ƙara da cewa bayan dawowar mataimakinsa daga jana’iza, ya shaida masa cewa ma’adinai suna ci gaba da kai wa jama’a hari a cikin gari.
Ya bayyana cewa rikici yana da illa, kuma Allah ba ya jin daɗin wanda ya tayar da shi, don haka aka baza jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yauri.













































