Hukumar Yaki da masu yi wa tattalin arzikin Kasa ta’annati (EFCC) ta kama Bashir Ibrahim, tsohon dan kwangilar gwamnatin jihar Kaduna, bisa zargin almundahana da ya kai Naira biliyan 30.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a ta X, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce Ibrahim, babban jami’in gudanarwa (CEO) na kamfanin Formal Act Legacy Limited, ana zarginsa da yin amfani da da’awar karya wajen yaudarar ‘yan kwangila da dama a Kaduna.
Hukumar ta ce, duk da dakatar da mu’amalarsa da gwamnatin jihar a hukumance a shekarar 2023, Ibrahim ya ci gaba da nuna kansa a matsayin mai ba da shawara ga kananan hukumomi 23 da ke Kaduna da kuma kungiyoyi irin su United Charity Foundation (UCF), FICCORD, da kuma Ofishin bunkasa muradun karni (SDGs).
“An kuma yi zargin cewa ya sanar da wadanda abin ya shafa cewa yana da yarjejeniyar fahimtar juna ta 2020, da gwamnatin jihar Kaduna, da nufin samo tallafin shiga tsakani daga hukumomin bada tallafi na duniya don tallafawa ayyukan karamar hukumar a jihar da kuma tallafawa aiwatar da SDGs a cikin jihar,” in ji sanarwar.
Hukumar ta ce bincike ya nuna cewa an kawo karshen zarginsa da gwamnatin jihar Kaduna a watan Oktoban 2023 bayan an same shi da saba ka’idojin da aka shimfida.
EFCC ta ce Ibrahim, duk da rashin goyon bayan da jami’ai suka bayar, ana zargin ya ci gaba da bayar da kwangiloli na biliyoyin Naira.
Karin karatu: EFCC ta kama tsohon dan majalisa Gudaji Kazaure bisa karbar Naira miliyan 70 daga hannun Emefiele
Hukumar ta kara da cewa Ibrahim ya karkata akalar kayayyakin ne domin amfanin kansa, ya sayar da wasu, sannan ya kasa kai ko bayyana wa kananan hukumomin da aka ce an sayo su.
Hukumar yaki da cin hancin ta kuma yi zargin cewa wanda ake zargin ya sayar da takardun kwangilar bogi ta hannun ‘yan tsaka-tsaki tare da raba musu kudaden da aka samu.
Haka kuma an kama kayayyakin magunguna kamar su capsules, syrups, creams, syringes, safar hannu, da alluran rigakafin yara, wadanda aka samu da yawa a wani dakin ajiya na sirri.”
Hukumar EFCC ta ce tana aiki da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) da ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna domin tantance lafiya da sahihancin magungunan da aka kwato.
Wani jami’in hukumar ta NAFDAC, Umar Suleiman, ya ce wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato wa’adin su sun kare, wasu kuma na jabu ne ko kuma na wasu kamfanoni da ba su yi rijista ba.
EFCC ta kara da cewa za a gurfanar da Ibrahim a gaban kotu da zarar an kammala bincike.













































